Labarai
INEC ta ce ta samu korafe-korafe 69 daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce ta samu korafe-korafe 69 daga jam’iyyun siyasa 12 a jihohi 26, dangane da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a babban zaben shekarar 2027, inda 41 daga cikin korafe-korafen suka yi nasara, yayin da aka yi watsi da 28.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis 29 ga Oktoba, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar, Mohammed Kudu Haruna.
INEC ta ce korafe-korafen sun shafi cire wasu jam’iyyun siyasa daga jerin sunayen ‘yan takara, shigar da sunayen mutanen da ba su cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu, da kuma zargin wasu ‘yan siyasa da samun tikitin tsayawa takara fiye da daya.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, ta samu korafe-korafe 61 daga jam’iyyun siyasa 11 a jihohi 11, dangane da ‘yan takarar majalisun dokokin jihohi, inda 25 suka yi nasara, yayin da aka yi watsi da 36.
INEC ta ce bayan nazarin korafe-korafen da kuma duba dokokin zabe da sauran bayanan da suka shafi lamarin, ta amince da shigar da sunayen wasu ‘yan takara da jam’iyyunsu da aka cire ba bisa ka’ida ba, tare da cire sunayen wadanda aka tabbatar ba sa cikin rajistar mambobin jam’iyyunsu.
Hukumar ta kara da cewa ta kuma cire wasu ‘yan takara da aka gano cewa takarar da aka tsayar da su bai cika sharuddan da doka ta tanada ba.
INEC ta ce za ta wallafa jerin sunayen da aka yi wa gyara, wadanda za su kunshi sunayen ‘yan takara da jam’iyyun da abin ya shafa, a shafinta na yanar gizo.
You must be logged in to post a comment Login