Labarai
Sojoji da ‘yan sanda sun ceto daliban da aka sace a Borno

Sojojin Operation HADIN KAI tare da jami’an ‘Yan Sandan Mopol sun dakile wani yunkurin harin mayakan ISWAP a Federal Government Girls College (FGGC) da ke Monguno a jihar Borno, inda suka ceto dalibai 46 ba tare da an yi garkuwa da ko guda ba.
Harin ya faru da misalin karfe 1:30 na safiyar Asabar, yayin da makarantar ke zama matsuguni na wucin gadi ga daliban Federal Polytechnic Monguno. Rundunar sojin ta ce maharan sun samu shiga makarantar ne da taimakon wasu da ake zargi da hada kai da su, amma jami’an tsaro sun yi gaggawar mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.
Sai dai rundunar ta bayyana cewa wasu dalibai sun rasa rayukansu sakamakon harbin da maharan suka rika yi yayin musayar wuta. Ta ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda ake zargin sun taimaka wa maharan, yayin da ake farautar wadanda suka tsere. Rundunar ta kuma jajanta wa iyalan wadanda suka mutu, tare da jaddada kudirinta na ci gaba da kare makarantu da sauran muhimman wurare a yankin Arewa maso Gabas.
You must be logged in to post a comment Login