Labarai
Wike ya tabbatar da ƙoƙarin ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, , ya tabbatar wa malamai da iyalan waɗanda aka sace cewa gwamnati na ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro domin ganin an ceto ɗalibai da malamai da ke hannun masu garkuwa da mutane.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da mambobin (NUT) suka gudanar da zanga-zanga a harabar Sakatariyar Hukumar Gudanar da Abuja domin nuna damuwa kan yawaitar hare-haren da ake kai wa makarantu da kuma sace ɗalibai da malamai a sassan ƙasar nan.
Rahotanni sun nuna cewa akalla ɗalibai 82 ne aka sace tsakanin ranakun 13 zuwa 15 ga watan Mayu a hare-hare daban-daban da suka faru a jihohin da . A Borno, an sace ɗalibai 42 bayan hare-hare a ƙananan hukumomin Askira Uba da Chibok, yayin da a Oyo aka sace wasu ɗalibai 40 daga makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Oriire.
Ministan ya ce yana da cikakken kwarin gwiwar cewa jami’an tsaro za su yi duk mai yiwuwa wajen ceto waɗanda aka sace cikin gaggawa. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji mayar da matsalar tsaro ta zama ta siyasa, yana mai cewa matsalar ta shafi kowa da kowa ba tare da la’akari da yanki ko jam’iyya ba.
You must be logged in to post a comment Login