Labarai
Amnesty International ta ƙaddamar da binciken gano masu ɗaukar nauyin faɗan daba a Kano

Kungiyar kare haƙƙin bilʼadama ta Amnesty International ta ƙaddamar da bincike don gano ƴan siyasa da ke daukar nauyin faɗace-faɗacen daba a Kano.
Babban Daraktan Kungiyar a Najeriya Malam Isah Sanusi, ya bayyana hakan a tattaunawarsa da kafar Arewa Updates.
Ya ce, tuni suka ƙaddamar da bincike a kan yawaitar faɗace-faɗacen daban da ke da alaƙa da ƴan siyasa.
Ya ƙara da cewa, da zarar sun kammala bincike za su kwarmata rahoton sunayen ƴan siyasar da aka gano suna da hannu wajen ɗaukar nauyin ayyukan dabar.
Amnesty ta kuma yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta ɗauki tsattsauran mataki domin yawaitar faɗan dabar zai iya firgita mutane da hana su shiga harkokin zaɓe balle su samu damar kaɗa ƙuriʼa.
You must be logged in to post a comment Login