Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta musanta kashe mutane 5 yayin rantsar da mataimakin Gwamna

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta kisan mutane biyar a jihar yayin rantsar da mataimakin Gwamna a ranar Talatar nan.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar.

Sanarwar tace binciken da gwamnati da jami’an tsaro suka gudanar bai tabbatar da faruwar lamarin ba, sakamakon gaza samun rahoto a hukumance.

Sanarwar ta bayyana cewa rikicin da ake zargin wasu ‘yan daba sun yi, bai faru a kusa da gidan gwamnati ba, saboda haka bai kamata a danganta shi da bikin gwamnatin jihar ba.

Gwamnatin ta kuma nuna takaicinta kan yadda kungiyar Amnesty International ta wallafa rahoton ba tare da tantancewa daga jami’an tsaro ko hukumomin gwamnati ba, inda ta zargi kungiyar da dogara da bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!