Labarai
CISLAC ta zargi jagororin siyasar Kano da ingiza matasa wajen aikata ta’addanci

Kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa da sanya idanu kan harkokin siyasa a Najeriya CISLAC, ta zargi jagororin siyasar Kano da ingiza matasa wajen aikata ta’addanci a jihar musamman a yayin tarukan siyasa.
Shugaban kungiyar Kwamred Auwal Musa Rabsanjani kuma shugaban kwamatin amintattu na kungiyar Amnesty International a Najeriya ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya kuma bayyana takaicinsa bisa yadda aka samu kisan wasu matasa a Kano sakamakon saɓani na siyasa.
Inda ya ce, kasashe da dama na yin amfani da matasansu wajen ci gaban kasar amma a Najeriya ana yin amfani da su wajen bangar siyasa da ba su kwayoyin da za su gusar da tunanin su.
You must be logged in to post a comment Login