Connect with us

Labarai

Amnesty ta yi Allah-wadai bisa kamawa tare da yanke hukunci daurin shekaru 4 ga Farida Isihak

Published

on

Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta yi Allah-wadai sakamakon kama tare da tsare wata ‘yar jarida mai shekaru 23, Farida Isihak, hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan gyaran hali ko kuma biyan tarar Naira miliyan 1.75 a jihar Kaduna.

Ƙungiyar ta bayyana hukuncin a matsayin wani mataki na ramuwar gayya da kuma yunƙurin hana ‘yan jarida gudanar da ayyukansu na fallasa zargin cin zarafin jama’a da wasu jami’an ‘yan sanda ke yi.

 

Amnesty International ta ce Farida Isihak, wadda ke aiki da gidan rediyon Nagarta da ke Jihar Kaduna, ta fuskanci hukuncin ne daga wata kotun Shari’a da ke Kawo, sakamakon zargin ɓata suna da ya biyo bayan wani saƙon da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta soki ayyukan ‘yan sanda.

 

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, ƙungiyar ta bayyana shari’ar a matsayin shari’ar da ba ta bi ƙa’ida ba, tare da yin Allah-wadai da abin da ta kira kame ba bisa ƙa’ida ba, tsarewa da kuma gaggawar yanke wa ‘yar jaridar hukunci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!