Connect with us

Labarai

Shirin CNG ya samar da Motocin Bas 670 a fadin Najeriya

Published

on

Shirin bunƙasa amfani da iskar gas a Najeriya, Decade of Gas da PI-CNG & EV, ya bayyana cewa an samar da motocin bas masu amfani da iskar gas ta CNG guda 670 a faɗin ƙasar, a wani mataki na rage kuɗin sufuri da bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta.

Shirin ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan ’yan jarida da Sakatariyar Decade of Gas, tare da shirin Shugaban Ƙasa na bunƙasa amfani da CNG da motocin lantarki, PI-CNG & EV, suka shirya a Kano ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026.

Jagoran Sashen Samar da Ababen More Rayuwa da Bunƙasa Amfani da Iskar Gas na Sakatariyar Decade of Gas, Mista Taofeek Balogun, ya ce Najeriya an samu ci gaba a ɓangaren iskar gas, inda adadin iskar gas ɗin da aka tabbatar ƙasar na da shi ya ƙaru daga tiriliyan 208.83 a shekarar 2023 zuwa tiriliyan 215.19 a watan Janairun 2026.

Ya ce, matsakaicin yawan iskar gas da ake hakowa ya ƙaru daga kusan biliyan 6.86 zuwa biliyan 7.5 a kowace rana, yayin da iskar gas da ake samarwa domin amfanin cikin gida ta haura biliyan biyu a kowace rana.

Balogun ya kuma bayyana cewa an samu alkawuran zuba jari na dalar Amurka biliyan 3.5 a manyan ayyukan iskar gas guda huɗu, yayin da aikin bututun iskar gas na OB3 ya kammala gaba ɗaya, na AKK kuma ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na kammalawa.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta ware naira biliyan 671 domin ayyukan samar da ababen more rayuwa, matakin da ya taimaka wajen jawo jarin masu zaman kansu da ya kai kusan naira tiriliyan 1.6.

Dangane da shirin samar da makamashin girki mai tsafta, Balogun ya ce shirin LPG na da burin samar da iskar gas ga gidaje miliyan biyar kafin shekarar 2030, inda aka fara aiwatar da wasu ayyuka a jihohin Bayelsa da Akwa Ibom tare da rarraba tankunan girki na LPG guda 27,000.

Ya kuma bayyana cewa Najeriya na shirin sauya tsarin kasuwar iskar gas zuwa tsarin da masu saye da masu sayarwa za su riƙa amincewa da farashi da yarjejeniyar ciniki, wanda aka fi sani da Willing Buyer, Willing Seller. Ya ce ana sa ran fara aiwatar da tsarin a ranar 24 ga Satumba, 2028, domin ƙarfafa gasa da gaskiya a harkokin kasuwancin iskar gas.

A nasa jawabin, babban jami’in gudanarwa na shirin PI-CNG & EV, Mista Tosin Coker, ya bayyana cewa amfani da CNG a motocin sufuri na da muhimmanci wajen rage kuɗin zirga-zirga, ƙarfafa tsaron makamashi da kuma bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta.

Coker ya kuma yi bayani kan damuwar da ake nunawa game da amincin amfani da CNG, inda ya jaddada muhimmancin amfani da cibiyoyin sauya motocin da aka amince da su, kayan aiki ingantattu, bin ƙa’idojin hukumomi da kuma kula da motoci yadda ya kamata.

A cewar shirin PI-CNG & EV, daga cikin motocin bas guda 670 da aka samar, guda 285 na gudanar da zirga-zirgar kasuwanci a jihohi 13, yayin da aka ware guda 302 domin ƙungiyoyin sufuri, ɗalibai da hukumomin gwamnati.

Shirin ya ce sauya motocin da ke amfani da man fetur zuwa CNG ya fi mayar da hankali kan motocin kasuwanci domin taimaka wa direbobi rage kuɗin makamashi da kuma sauƙaƙa kuɗin sufuri ga fasinjoji.

Ya ƙara da cewa a ƙarƙashin shirin National Affordable CNG Transition Programme, an samu raguwar kuɗin mota daga kashi 15 zuwa kashi 50 a wasu hanyoyin da motocin bas masu amfani da CNG ke bi.

Haka kuma, ana shirin gina ƙarin tashoshin cika CNG guda 127 a jihohi 31 da Babban Birnin Tarayya, Abuja, domin faɗaɗa damar samun iskar gas ga masu amfani da ita.

Dangane da jihar Kano, shirin ya bayyana ta a matsayin muhimmiyar cibiyar bunƙasa sufuri mai amfani da makamashi mai tsafta a Arewacin Najeriya.

Bayanin ya nuna cewa Kano ce ke kan gaba a yankin Arewa maso Yamma, inda take da tashoshin cika CNG guda bakwai da ke aiki, yayin da ake ci gaba da kammala wasu tashoshi guda 17.

Haka kuma, shirin ya samar da ƙarin motocin bas guda 25 a jihar Kano domin ƙarfafa amfani da CNG a harkokin sufuri.

An bayyana cewa waɗannan matakai na da nufin samar da sufuri mai araha, jawo zuba jari da kuma bunƙasa masana’antu a Arewacin Najeriya.

Taron wayar da kan da aka gudanar a Kano ya samu halartar ’yan jarida 27 daga gidajen talabijin, rediyo, jaridu da kafafen yaɗa labarai na zamani.

Masu shirya taron sun ce wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan taro ga ’yan jarida a Kano, bayan tarukan da aka yi a Legas, Abuja da Fatakwal.

A yayin taron, ’yan jarida sun gabatar da tambayoyi kan yadda ake samar da iskar gas, farashinta, amincin amfani da ita, bunƙasa ababen more rayuwa da kuma aiwatar da manufofin gwamnati a wannan fanni.

Da yake magana a madadin mahalarta taron, Murtala Adewale na jaridar The Guardian ya yaba wa Sakatariyar Decade of Gas da shirin PI-CNG & EV bisa shirya taron, yana mai bayyana shi a matsayin mai ilmantarwa da faɗaɗa fahimtar ’yan jarida.

Ya yi kira da a riƙa shirya irin waɗannan taruka akai-akai, tare da ƙara yawan ’yan jaridan da za su halarta da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki a masana’antar iskar gas.

A ƙarshe, Sakatariyar Decade of Gas da shirin PI-CNG & EV sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kan manufofi da shirye-shiryen bunƙasa amfani da iskar gas a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!