Labarai
PRP ta yi gargaɗi kan zargin shirin haddasa rarrabuwar kai a tsakanin mambobinta

Jam’iyyar PRP ta yi gargaɗi kan zargin shirin haddasa rarrabuwar kai a cikinta, da nufin raunana damar da take da ita a lokacin zaɓe da kuma ƙoƙarin haɗa kan jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta zargi wasu tsoffin mambobinta da wasu jami’an da ke aiki a cikinta da ƙoƙarin haddasa rikici da kuma lalata goyon bayan da take samu daga magoya bayanta tun daga tushe.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi zargin cewa waɗanda ke da hannu a shirin na neman kashe ɗaruruwan miliyoyin naira domin sayen goyon bayan mambobi da kuma ƙirƙirar wani ɓangare na daban a cikin jam’iyyar.
Sai dai PRP ba ta bayyana sunayen mutanen da take zargi ba, haka kuma ba ta gabatar da hujjojin da za su tabbatar da zarge-zargen a cikin sanarwar ba.
Baba-Ahmed ya buƙaci mambobin jam’iyyar da sauran jama’a da su yi tsayin daka wajen hana faruwar hakan da ya kira yunƙurin rusa jam’iyyar, musamman batun ɗaukar wakilan rumfunan zaɓe, da wasu da basu da ikon yin hakan ke kokarin yi
You must be logged in to post a comment Login