Ƙetare
Amurka da Iran na iya sake komawa kan teburin tattaunawar sulhu

Ana hasashen cewa Amurka da Iran na iya sake komawa kan teburin tattaunawar sulhu cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da jaridar New York Post, inda ya ce akwai yiwuwar samun wani ci gaba nan da kwanaki biyu, tare da nuna cewa Pakistan na daga cikin wuraren da ake dubawa domin gudanar da tattaunawar.
Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da bangarorin biyu suka yi a karshen makon da ya gabata a Pakistan.
A lokacin, mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ne ya wakilci kasar, yayin da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, da wasu jami’an kasar suka jagoranci tawagar Iran.
To sai dai, duk da tattaunawar da aka yi, ba a cimma wata yarjejeniya ba a tsakanin bangarorin.
You must be logged in to post a comment Login