Labarai
Kotun koli ta sanya 22 ga watan Afrilu domin shari’ar ADC

Kotun kolin kasar nan ta sanya ranar 22 ga watan Afrilun da muke ciki domin sauraron karar da shugaban jam’iyyar ADC na kasa, David Mark, ya shigar gabanta dangane da rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar.
Karar na da alaka da shari’ar da wani tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Nafiu Bala, ya gabatar, wadda ta haifar da takaddama a tsakanin bangarorin biyu.
Ana sa ran sauraron shari’ar zai ba da haske kan wanda ke da hurumin shugabantar jam’iyyar, yayin da rikicin ke ci gaba da jan hankali a fagen siyasar kasar.
Hukuncin da kotun za ta yanke na iya zama mai tasiri sosai ga makomar jam’iyyar ADC da kuma tsare-tsarenta a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login