Ƙetare
Amurka ta zargi Afirka ta Kudu da taimaka wa Rasha da makamai
Kasar Amurka ta zargi Afirka ta Kudu da taimaka wa kasar Rasha da makamai domin amfani da su wajen mamayar kasar Ukraine, duk da ta bayyana matsayin ta na ‘yar ba ruwan ta a cikin wannan rikici.
Jakadan Amurka a Afirka ta Kudu Ambasada Reuben Brigety ya bayyana cewar a watan Disamba Shekarar da ta gabata, inda akaga lokacin da Afrika ta Kudu tayi lodin Makamai a gabar jirgin ruwan Cape Town domin aikewa da su zuwa Rasha .
Kasar Afrika ta Kudu taki fitowa fili ta soki matakin da Rasha da mamaye Ukraine wanda ya haifar da takun saka tsakanin Kasashen Yammacin Duniya a gwamanatin Vladimir Putin
You must be logged in to post a comment Login