Labarai
An binne marigayi tsohon shugaban kasar Zambia
An kammala jana’izar tsohon shugaban kasar Zambia wanda ya jagoranci karbo ‘yancin kasar, Kenneth Kaunda inda aka birne shi a makabartar da ake binne manyan shugabannin kasar duk da kin amincewar hakan daga ‘yan uwansa.
Gabanin fara jana’izar alkalin babbar kotun kasar, Wilfred Muma ya ki amincewa da bukatar a birne shi a gonarsa, ya na mai cewa Kaunda na daga cikin muhimman mutanen da ake alfahari da su a kasar, don haka za a binne shi a inda ya dace.
Hakan ta sanya gwamnatin kasar ta bayar da umarnin gudanar da bikin jana’izar a Embassy Park, wata makabarta ta alfarma da aka kebewa shugabannin kasar.
Wasu daga cikin dangin marigayin dai sun so a binne shi a wata gonarsa kusa da inda aka birne matarsa Betty.
Dubban mutane ne a kasar ke bayyana alhinin mutuwar Kaunda da ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 97 a Duniya, wadanda ke bayyana shi a matsayin mai fafutuka dan gwagwarmaya kuma malami wanda ya kamata ayi koyi da shi.
Shugaba Edgar Lungu ya bayyana ranar haihuwar Kaunda, 28 ga Afrilu, a matsayin ranar hutu don girmama shugaban kasar na farko kuma dan fafatuka wanda ya yi gwagwarmayar kwato ‘yancin kasar.
You must be logged in to post a comment Login