Labaran Kano
An bude sabbin filayen noman rani a jami’ar Bayero
Ministan noma da raya karkara, Alhaji Sabo Nanono ya bude sababbin filayen noman rani, wanda cibiyar bincike kan noma a tsandauri ta jami’ar Bayero dake Kano ta shirya.
Da ya ake jawabi a wajen taron Ministan ya jaddada kudurin gwamnatin tarayya na ci gaba da bunkasa bangaren noma a kasar nan musamman ma manoman rani don samar da abinci da kayan marmari tare da bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Alhaji Sabo Nanono ya kara da cewa akwai ayyukan noma masu yawa da gwamnatin tarayya ke bullowa da su, musamman ma a bangaren samar da filayen noman rani tare da tallafawa manoma musamman ma mazauna yankunan karkara.
Shugaban jami’ar ta Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya ce jami’ar na kokarin karfafawa manoma ta bangaren bincike don saukakawa manoma gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Shi kuwa Daraktan cibiyar, Farfesa Jibril Muhammad Jibril cewa ya yi cibiyar ta horar da masu karatun digiri na biyu sama da dubu biyu daga kasashe goma-sha-uku a bangaren noma.
Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan malaman jamia daga ciki da wajen kasar nan da sauransu.