Labaran Kano
An bukaci matasa su rungumi sana’o’in dogaro da kai
Dan masanin Kano Alhaji Abdullakadir Yusuf Maitama Sule ya ja hankalin matasa dasu tashi su nemi na kansu su daina dogara akan gwamnati sai basu aikin yi.
Alhaji Abdullakadir ya bayyana haka ne lokacin da yake bude wani sabon ofishin sayar da kayan gine-gine dake kan titin Lodge Road dake tsakiyar birnin Kano.
Ya ce yanzu lokaci ya wuce da matasa zasu rika bata lokacin suna yin abubuwan da basu dace ba musamman shaye-shaye, inda ya bukaci matasa da su rungumi sana’o’i domin tallafawa kansu tare da ragewa gwamnati nauyin samar da aikin yi.
Ya kuma yabawa matashin da ya bude wannan shagon, tare da yin kira ga sauran matasa da su jajirce wajen yin sana’o’in dogaro da kai.
A nasa bangaren wanda ya bude shagon na sayar da kayan gine-gine Injiniya Khalifa Rabi’u ya ce ya yi wannan kokari ne domin taimakawa kansa da kuma sauran mutane da suke tare da shi, inda ya bayyana cewa zai yi kokari wajen ganin ya bunkasa shagon har ya kai matakin kamfani.
Wakilinmu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito matasan na kira da gwamnati da ta ci gaba da basu hadin kai wajen bunkasa sana’o’in da suke yi wanda hakan zai taimaka wajen samar da aikin yi ga sauran ‘yan uwansu matasa.