Labaran Wasanni
An cafke Ronaldinho a kasar Paraguay bisa zargin fasfon bogi
Hukumomi a kasar Paraguay, sun kama tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Brazil, Ronaldinho bisa zargin sa da amfani da fason Bogi tare da shiga kasar ba bisa ka’ida.
Mai shekaru 39, Ronaldinho, wanda ya lashe kofin duniya da kasar sa a shekarar 2002, kasashen Japan da Korea, an kama shi ne a wani gurin shakatawa na bakin Tafki,mai suna Resort Yacht & Golf Club Paraguayo, tare da dan uwansa Roberto, a daren jiya Laraba, kamar yadda sanarwar ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Paraguay ta tabbatar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an samu fasfo din a dakin su na Otal, dashi da dan uwansa da sunayen su a jikin fasfo na kasar ta Paraguay.
Labarai masu alaka.
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
Shin kun san alkalin da zai busa wasan Nijeriya da Brazil?
Bayanai daga wajen ‘yan sandan kasar ta Paraguay, sun tabbatar da cewa Ronaldinho, da dan uwansa sun shigo kasar ne bisa gayyatar wani gidan rawa da shugaban sa Nelson Belotti, ya, yi musu don gabatar da tsohon dan wasan tare da ganawa da dumbin magoya baya, da ‘yan jaridu da masu ruwa da tsaki a kwallon kafar kasar.
A baya hukumomi a kasar Brazil, sun zargi dan wasan da, dan uwan sa da yin gini ba bisa ka’ida ba a gefen kogi na Guaiba,a shekarar 2015, wanda waje ne da a ke kamun kifi , ba tare da samun lasisin yin haka ba, hakan ta sa a ka ci su tarar sama da fam miliyan shida, kimanin naira biliyan ashirin da takwas.
Hakan ta sa aka kwace fasfon shi na kasar Brazil a watan Nuwambar shekarar 2018, tare da hana shi tafiye tafiye, sakamakon kin biyan tarar kamar yadda babbar kotun kasar Brazil ta nema.
You must be logged in to post a comment Login