Jigawa
An cafke wasu matasa da ake zargi da yin fashi a Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu matasa guda 4 da ake zargi da aikata fashi da makami a ƙaramar hukumar Malammadori.
Rundunar tace ta karbi korafi daga wani magidanci mai suna Muhammad Sani Abubakar mazaunin unguwar Yayari a garin Hadejia, wanda yace wasu fulani sun tare su ɗauke da makamai sun ƙwace musu wayoyin hanu har guda 3, da kuma kuɗi naira dubu 6 ya yin da suke kan hanyar su ta komawa gida daga gona shi da ɗan uwansa.
Bayan da jami’an ‘yan sandan suka fara gudanar da aikin bincike, sun samu nasarar kama wani mutum mai suna Muhammad Abdullahi mai sana’ar sayar da wayoyi a wata rigar fulani dake yankin ƙaramar hukumar Kirikasamma, sakamakon samun sa da wayoyin da aka yi fashin su.
Faruwar hakan dai tasa jami’an sun sake kamo wasu matasa, wadan da ake zargi da aikata laifin yin fashin, da suka hada da wani mai suna Abdullahi Abubakar mai shekaru 25, da kuma Sulaiman Abdullahi mai shekaru 20, sai kuma na 3 Abdullahi Mammam mai shekaru 20, wadan da dukkan su’yan rigar mushimbiba ne ta karamar hukumar Malammadori a jihar Jigawan.
Rundunar tace aikata irin wannan laifi ya sabawa sashi na 96 da 296 da kuma 316 na kundin hukunce-hukuncen final code.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri, na cewa, nan gaba kaɗan zasu gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya.
You must be logged in to post a comment Login