Connect with us

Labaran Kano

An fara sauraran karar mutane 3 da ake zargi da hada baki wajen kisan kai -Kotu

Published

on

Kafin zaman kotun na yau gwamnatin Kano dai na zargin mutanen da laifin hada baki da kisan kai, laifukan da suka saba da sashi na 97 dana 221 na kundin penal code na kasar nan.

Babbar kotun jiha mai lamba 9 karkashin mai Shari’a Aisha Mahmud ta fara sauraron shaidu cikin kunshin zargin da gwamnatin jaha take yiwa wasu mutane uku.

Da yake jawabi Lauyan gwamnati Lamido Abba Soron dinki ya gabatar da takaddar tuhumar a gaban kotu wanda kunshin ta ya bayyana cewar mating Joseph da wani mai suna Tahir Tanimu da Aminu Yahaya sun hada baki sun hallaka wani mai suna shamsu yakubu a ranar 1/3 2019 sakamakon hargitsin siyasa.

Sai dai wadanda ake zargin sun musanta mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu uku an kuma sanya ranar 17 ga watan gobe dan ci gaba da sauraron shaidun masu kara wakilinmu Yusuf Nadabo ya so jin ta bakinsu sai dai sun ki cewa komai

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!