Labarai
An fara sayar da hannun jarin kamfanin Mai na Dangote

An buɗe hannun jari mafi girma a Afirka ga jama’ar da ke da sha’awar siyan hannun jari a matatar mai ta Dangote.
Matatar ta Ɗangote tana tayin sama da hannun jari biliyan huɗu a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake sa ran za ta samar da kusan dala biliyan 1.6.
Matatar ta ƙara da cewa tana son bai wa jama’a damar kasancewa masu hannun jari a matatarsa da ta soma aiki shekaru biyu da suka gabata kuma tuni ta kasance matata mafi girma a nahiyar Afirka.
Dangote ya bayyana cewa yana shirye-shiryen faɗaɗa aiki a matatar da za a kashe dala biliyan 14 wanda zai ruɓanya ayyukan matatar nan da shekarar 2029.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin fetur ya kusa kaiwa naira dubu daya da dari hudu kan kowace lita zuwa ƙarshen watan Agusta a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login