Labarai
Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani ya zama sabon Sarkin Gumel na 17

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya naɗa Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin sabon Sarkin Gumel na 17, bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Dr. Ahmed Muhammad Sani II.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim ya fitar, ta ce naɗin ya biyo bayan shawarar masu zaɓen sarki na masarautar Gumel da Majalisar sarakunan Jihar Jigawa.
Mahaifin sabon sarkin ya rasu ne ranar Alhamis, 3 ga Satumba, 2026, bayan shafe shekaru 46 yana mulkin masarautar Gumel.
Kafin naɗinsa, Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani shi ne Chiroman Gumel, kuma yana aiki a matsayin daraktan Tsaron Intanet na Hukumar NITDA.
Gwamna Namadi ya kuma gode wa masu zaɓen sarki da sarakunan Hadejia, Kazaure, Ringim da Dutse bisa gudunmawarsu wajen zaɓen sabon Sarkin.
You must be logged in to post a comment Login