Ƙetare
An fara zaman makoki na kwanaki 3 a Libiya bisa rasuwar babban hafsan sojin kasar

An ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar Libiya, kan abun da aka kira da babbar asarar da kasar ta yi wacca zai yi wuya a iya maye gurbinta.
Tuni tawagar binciken kwakwaf ta kasar ta Libiya ta isa birnin Ankara na kasar Turkiya, domin gudanar da nata binciken kan hakikanin musabbabin mutuwar marigayi Laftanar Janar Mohammad al-Haddad da masu dafamar baya su shida.
Ma’aikatar cikin gidan Turkiyya dai, ta sanar da gano burakuzan jirgin da gawarwakin mamatan gami da bakin akwatin jirgin saman da ya yi hadari da janar din, kamar yadda ministan ma’aikatar cikin gidan Turkiyya Ali Yerlikaya ya nuna hotunan da tauraron dan Adam ya dauka na hadarin jirgin.
Firaministan Libiya Abdul Hamid Dbeibeh ya sanar da rasuwar babban hafsan sojin kasar da wasu manyan jami’an sojin kasar, sakamakon mummunan hadarin, yayin da suke komawa gida daga wata ziyarar aiki a Turkiyya kamar yadda ya wallafa bakin cikinsa a shafinsa na X.
You must be logged in to post a comment Login