Coronavirus
An gano karin masu cutar Corona 403 a Najeriya
Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta tabbatar da samun karin mutane 403 dake dauke da cutar Coronavirus a jihohi 19 na kasar nan da kuma birnin tarayya Abuja.
Cikin sanarwar da hukumar ta NCDC ta fitar a daren Lahadi tace jihar Gombe ce ke kan gaba a yawan masu dauke da cutar a ranar Lahadi wadda take da mutane 73 sai jihar Legas mai mutum 68.
Jihar Kano na mataki na uku da mutane 46, Jihar Edo mutum 36, sai birnin tarayya Abuja mai mutane 35, jihar Nasarawa mutum 31, sai 17 a jihar Kaduna.
Jihar Oyo an samu karin mutum 16 sai jihar Abia mutum 15, a jihohin Delta da Borno na samu karin mutane goma sha uku kowannen su.
A jihar Plateau an samu karin mutum 8, jihar Niger mutum 7 sai jihar Rivers ita ma mutum 7, aa jihar Enungu mutum 6, hakama a jihar Ogun mutum 6, jihar Kebbi an samu karin mutum 3.
Jihohin Ondo da Anambara da kuma jihar Oyo an samu karin mutum dai-dai kowaccen su.
Yazuwa yanzu NCDC tace mutane 16,085 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.
Mutum 5,220 daga ciki sun warke daga cutar, yayin da 420 daga ciki suka rasa ransu sanadiyyar cutar.
You must be logged in to post a comment Login