Coronavirus
An gano karin mutane 14 dauke da cutar Covid-19 a Jigawa
Hukumomi a jihar Jigawa sun tabbatar da samun karin mutane 14 da sakamakon gwajinsu ya nuna cewa suna dauke da cutar Coronavirus.
Shugaban kwamatin dakile yaduwar cutar na jihar Jigawa Dakta Abba Umar ne ya bayyana hakan, inda yace 10 daga cikin adadin wadancan mutane almajirai ne da jihar Nassarawa ta dawowa da Jigawa, yayin da biyu kuma suka fito daga Dutse sai daya daga Gumel.
Haka kuma kwamishinan yace sauran mutum daya kuma an same shi ne a kauyen Bule ta karamar hukumar yan kwashi, wadda daga 12 na daren ranar juma’a za a rufe kauyen na tsawon mako guda.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 225 a jahar jigawa.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kwaminshinan na cewa cikin wancan adadi tuni mutane 81 suka warke, yayin da 3 suka yi shahada.
Ya zuwa yanzu dai mutane 141 ne ke killace karka shin kulawar likitoci kuma basa cikin halin damuwa.
Karin labarai:
Covid-19: Cibiyar gwajin Corona zata fara aiki a Jigawa
You must be logged in to post a comment Login