Connect with us

Labarai

NiMet ta yi hasashen samun  tsawa da ruwan sama a jihohi 10 na Arewacin Najeriya

Published

on

Hukumar hasashen yanayi ta kasa  NiMet ta yi hasashen samun  tsawa tare da saukar ruwan sama a jihohi 10 na Arewacin kasar da kuma wasu jihohin Kudancin kasar, a yau Lahadi.

Wannan na kunshe ne a cikin hasashen yanayin da hukumar ta fitar a shafinta na X a yammacin  jiya Asabar.

 

Hasashen ya nuna cewa za a samu bullar hasken rana a Arewacin ƙasar a safiyar Lahadi, kuma ranar za ta iya zuwa da zafi, ta ce ana sa ran samun tsawa da ruwan sama a wasu sassa na kudancin jihar Adamawa da Taraba tun da safiyar da ta gabata.

 

NiMet ta ce za a samu ruwan sama a Abuja da jihohin Nasarawa, Plateau, Benue, Kwara da Kogi a yammacin yau Lahadi.

 

Ya yin da ta ce a  kudancin ƙasar kuwa, yanayin zai kasance mafi tsanani inda za a samu ruwan sama kusan a dukkan jihohin yankin, ciki har da Akwa Ibom, Rivers, Cross River, sai da  yammacin ranar  za a samu ruwan sama a Lagos, Ogun, Oyo, Osun, Ekiti, Ondo, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, Akwa Ibom, Abia, Imo, Anambra, Enugu, Ebonyi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!