Labarai
An garkame Sadiya Haruna a gidan yari
Rahotanni sun bayyana cewar,Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai sharia Muntari Garba Dandago ta aike da wata mata mai suna sadiya Haruna gidan gyaran hali.
Kazalika tun da farko ‘yansanda ne suka gurfanar da ita bisa zargin bata suna laifin da ya saba da sashi na 391 na kundin hukunta masu laifin Penal code.
A yayin zaman kotun mai shari’a Muntari Garba ya karantu Kunshin tuhumar ya bayyana cewar wani mashiryin shirin Hausa mai suna Isa A Isa shine yayi korafin akan cewar sadiyar ta bata masa suna.
bayan da aka karanta kunshin tuhumar sadiyar ta musanta zargin lauyan da yake kareta.
Har’ila yau, lauyan wacce a ake kara Y A Sharif ya roki a sanya ta a hannun beli ya ya buga misali da sashi na 35 da na 36 na kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyaran fuska a shekarar 2011 .
Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna
Abinda ya sanya ba zan iya auren Yawale a zahiri ba -Rayya
Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood
Sai dai mai gabatar da kara Jacob ya yi suka inda ya bayyanawa kotun cewar da zarar an bayar da belin wadda ake zargin za ta iya kawo tarnaki a binciken da ‘yansanda sukeyi ko kuma ta tserewa shari’a.
Mai sharia Muntari Dandago ya sanya ranar juma’a dan yin kwarya kwaryar hukunci akan rokon beli ya kuma yi umarnin a tsare ta zuwa waccan rana.
Wakilin mu Yusuf Naabo Isma’il ya zanta da mai kara ISa A Isa Wanda yayi Karin haske kan zargin da Sadiya tayi masa.
Duk wani yunkuri da wakilin namu yayi dan jin ta bakin sadiyar abin ya faskara sai dai a cikin kotun ta bayyanawa alkalin cewar wannan zargi bashi da tushe, balantana makama.