Kiwon Lafiya
An gurfanar da uba da ‘yarsa gaban kotu bisa zargin shirya auren bogi
An gurfanar da wani magidanci mai shekaru sittin mai suna Inusa Aliyu da ‘yar sa Jamila Aliyu gaban wata babbar kotun shiyya da ke da zama a Unguwar Masaka a jihar Nassarawa sakamakon zarginsu da laifin shirya auren bogi ga wani mutum mai suna Yusuf Mamuda.
Mutanen biyu da ake zargi mazaunan Unguwar Luvu da ke garin Masakan jihar Nassarawa mai iyaka da birnin tarayya Abuja, ana zargin su da aikata laifuka uku wajen hadin baki da kuma zamba cikin aminci.
Dan sanda mai gabatar da kara Frank Swem, ya shaidawa kotun cewa, wani mutum mai suna Yusuf Mamuda mazaunin Unguwar Kurudu a birnin tarayya Abuja, ya shigar da kara a ofishinsu da ke Masaka a ranar hudu ga watan da muke ciki na Janairu yana zargin mutumin da ‘yar sa Jamila da hada baki wajen shirya masa auren bogi.
A cewar sa a wata rana cikin watan Satumba a shekarar da ta wuce wani mutum mai suna Haruna wanda yanzu haka ya tsere, sun hada baki da mahaifin yarinyar Inusa Aliyu inda suka bukace shi da ya auri Jamila.
A cewar dan-sanda mai shigar da karar mutanen biyu sun bukaci Yusuf Mamuda da ya biya kudi naira dubu dari shida da hamsin domin a daura mashi aure da Jamila, kudaden da ya ce batare da bata lokaci ba ya biya su, sai dai daga bisani ya gane cewa mutanen damfarar sa suka yi, zargin da mutanen biyu suka musanta.
Da ya ke gabatar da hukunci alkalin kotun Yakubu Ishaku, ya bayar da belin mutanen biyu akan kudi naira dubu dari biyar-biyar, da kuma gabatar da mutum dai-dai wadanda zasu tsaya musu. Kafin daga bisani kuma ya daga karar zuwa ranar sha tara ga wannan wata da muke ciki.