Labarai
Za’a buɗe ofisoshin jami’an tsaro mallakin jihar Kano a ƙananan hukumomi 44

Gwamnatin Jihar Kano ta ce a mako mai zuwa za a fara buɗe ofisoshin jami’an tsaro mallakin jihar a dukkanin ƙananan hukumomi arba’in d hudu domin ƙarfafa harkokin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar tare da samar musu da kayan aiki.
Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarautu, Alhaji Tajuddeen Uthman, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da Freedom Radio.
Tajuddin Uthman ya ce kafa ofisoshin jami’an tsaron wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta tsaro a matakin ƙananan hukumomi tare da samar da tsarin da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro cikin gaggawa.
Alhaji Tajuddeen Uthman ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen da suka dace domin fara aiki da ofisoshin, inda ya ce za su kasance cibiyoyin da za su taimaka wajen tattara bayanan sirri, sa ido kan al’amuran tsaro da kuma haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma jihar.
You must be logged in to post a comment Login