Labarai
NAHCON ta kammala jigilar maniyyatan bana

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta sanar da kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana zuwa ƙasar Saudiyya.
Hukumar ta ce an kammala jigilar ne bayan jirgin ƙarshe na kamfanin Max Air da ya tashi daga filin jirgin saman Gusau ɗauke da Mahajjatan jihar Zamfara, a yau.
NAHCON ta bayyana cewa an kammala tashin jiragi na 98 cikin kwanaki 18, inda Nijeriya ta samu guraben maniyyata 50,000 a Hajjin bana.
You must be logged in to post a comment Login