Labaran Kano
An karrama Nasiru Zango
Kungiyar daliban yammacin Afrika, ta karrama shugaban sashen al’amuran yau da kulum na Freedom Rediyo, Nasir Salisu Zango, bisa yadda yake jajircewa wajen samarwa da al’umma mafita a fadin Kano da ma Nijeriya baki daya.
A yayin mika Lambar yabon, shugaban kungiyar shiyar Nijeriya, Mudassir Sabo Sadik, ya ce ba wani abu bane ya sanya su karrama Nasir Zango, illa kawai yadda yake fadi tashi wajen samar da mafita ga al’umma wajen fayyace gaskiya da gaskiya.
Ya kuma ce ba wai kawai suna baiwa mutum lambar girmamawa sai don su kara masa karfin gwiwa.
RUBUTU MASU ALAKA:
Ina yabawa ‘yan sandan jihar Kano –Magajin garin Daura
Mahukunta sun rufe makarantar KCC Kano
Mudassir Sabo Sadik, ya kuma kara da cewar sauran ‘yan jarida da su kasance masu gaskiya da rikon amana domin duk abin da mutum zai yi a rayuwar duniya har idan ba ka yi gaskiya ba ba kai ba cigaba.
A nasa jawabin, shugaban sashen al’amuran yau da kullum na Freedom Rediyo, Nasir Salisu Zango, ya ce komai kankantar karramawa babace a wurin sa don kuwa ba a bada Lambar girma ta gazawa ana bada Lambar yabo ne ga mutanen da aka ga sun jajirce akan aikin su.
Ya kuma yabawa kungiyar bisa yadda suka zakulo irin aikin da yake harma suka ga ya dace da su karramashi.