Labarai
An rantsar da Hajiya Hauwa Umar a matsayin shugabar Akantoci mata
An rantsar da shugaba a kuma sauran jagororin ƙungiyar Akantoci mata ta Nijeriya SWAN shiyyar Kano.
Yayin bikin rantsuwar wanda ya gudana a tsakiyar birnin Kano, sabuwar shugabar ƙungiyar Hajiya Hauwa Umar FCA, ta sha alwashin tallafa wa ƴaƴa mata da tallafin karatu kyauta domin samun ƙarin ƙwararrun Akantoci a faɗin ƙasar nan.
Shan rantsuwar kama aikin nata dai ya tabbatar da ita a matsayin shugabar ƙungiyar wadda ta kasance ta biyu tun bayan kafuwarta.
Shugabar ƙungiyar mata Akantocin, ta ce, baya ga bayar da tallafin karatu da ta ƙuduri aniyar yi musamman ga ƴaƴa mata, haka kuma za su taimaka ta fuskar ƙarfafa wa masu shirin zama mambobin ƙungiyar musamman wajen ganin sun samu nasara a jarrabawar da ake rubuta wa.
Ita kuwa a nata ɓangaren, uwargida Misis Christiana Oluranti Danladi, wadda ta sauka daga shugabancin ƙungiyar bayan ƙarewar wa’adinta, ta bayyana cewa ta samu nasarori da dama cikin har da rabon tallafin kayan sana’o’in dogaro da kai ga fiye da mata 150.
Shi kuwa Sanatan Mazaɓar Adamawa ta tsakiya Sanata Aminu Iya Abbas, da ya halarci taron, wanda shi ma mamba ne a ƙungiyar ƙwararrun akantoci ICAN, ya buƙaci masu son zama ƙwararrun Akantoci da su dage wajen ganin sun cimma burinsu.
Yayin taron, ƙungiyar ta raba kyautuka ga wasu muhimman mutane da kuma wasu mambobinta.
You must be logged in to post a comment Login