Connect with us

Labarai

Hukumar Kare Hakkin Masu Saye ta Kano ta kama magungunan kwari da wa’adin su ya kare

Published

on

Hukumar kare Hakkin masu saye ta jihar kano KCPC, ta kama kimanin katan 419 na magungunan kwari da wa’adin amfani da su ya kare, a wani wuri da ke kan Titin Club Road a nan Kano.

 

Hukumar ta ce samamen ya biyo bayan samun bayanan sirri cewa an tara magungunan a wurin, tare da zargin cewa ana kokarin sauya musu yanayi ko mazubi domin sake mayar da su kasuwa.

 

Daraktan wayar da kai na hukumar, Jamilu Mustapha Yakasai, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun rufe wuraren da ake ajiye magungunan, yayin da ake ci gaba da bincike domin daukar matakin doka.

 

Shugaban hukumar Dr. Ibrahim Garba Muhammad, ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu sanya ido, tare da kai rahoton duk wani samfurin da suke zargin bai dace da amfani ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!