Labarai
An ci Kungiyar Nassarawa United tarar Naira Miliyan 6

Hukumar shirya gasar Firimiya ta kasa, NPFL,ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United Naira Miliyan shida, bayan da suka gaza samar da cikakken tsaro a wasan mako na 33 da suka buga da Plateau United.
Haka zalika hukumar ta NPFL ta dauke kungiyar daga buda wasanta na gida zuwa filin wasa na Pantami dake jihar Gombe, inda zasu buga ragowar wasannin su.
Sai dai kungiyar dake garin Lafia tana da awanni 48 don daukaka kara.
You must be logged in to post a comment Login