Labaran Kano
An samar da kwalejin kirkire-kirkire da fasaha don bunkasa fasaha – Darakta
Kwalejin kirkira da fasaha ta jihar Kano, ta bayyana cewa an samar da ita ne da nufin kara bunkasa fasahar kirkira da zane-zane don baiwa matasa damar dogara da kan su.
Daraktan kwalejin Malam Mustapha S. Mu’azu ne ya bayyana hakan ta cikin shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar freedom rediyo da ya mayar da hankali kan fasahar kirkira.
Malam Mustapha Mu’azu ya kara da cewa, kasancewar asalin makarantar ta al’kur’ani ce amma aka zamanantar da ita, ta yadda ake koyar da harkokin fasaha da kirkira, musamman ga matasa.
Malamin ya kuma kara dacewa shiga kwalejin ba’a bukatar wani mataki na karatu kafin shiga makarantar.
Sai dai yace kwalejin zata fara bada takardar shedar Digiri wanda hadin gwiwa ne da jami’ar karutu daga gida wato NOUN.
You must be logged in to post a comment Login