Coronavirus
An samu ɓullar sabuwar cutar corona samfurin Omicron
Cibiyar daƙile yaduwar cuttuka ta ƙasa NCDC ta tabbatar da ɓullar cutar corona samfurin Omicron a Najeriya.
NCDC ta ce, a yanzu mutane uku sun kamu da cutar bayan da aka yi musu gwaji.
Shugaban cibiyar Dr Ifedayo Adetifa ne ya sanar da hakan, yana mai cewa za a sanya ido kan matafiyan da ke shigowa kasar nan don daƙile yaɗuwarta.
A cikin wata sanarwar NCDC ta fitar a shafinta na sada zumunta ta ce wadanda suka kamu da sabon nau’in cutar corona na Omicron suna cikin matafiyan da suka dawo daga ƙasar Afrika ta Kudu a makon da muke ciki.
Sanarwar ta kuma ce duk da cewa mutanen na dauke ƙwayar da cutar amma ba su fara nuna almaun kamuwa da cutar ba, amma an wuce da su asibiti inda suke samun kulawar da ta kamata.
NCDC ta bayyana damuwa kan yadda cutar corona samfurin Omicron ke ci gaba da yaɗuwa a ƙasashen duniya.
A farkon makon da muke ciki ne aka bayyana ɓullar sabon nau’in cutar ta Omicron a kasar Afrika ta Kudu, abin da ya wasu kasashe irin su Birtaniya da Amurka ɗaukar matakin hana tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke kudancin Afrika.
You must be logged in to post a comment Login