Labarai
An samu cikakken tsaro da zaman lafiya a Najeriya-Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a yanzu haka an samu tsaro da kuma zaman lafiya duk da yan kunji-kunjin na bangaren tsaro da ake fuskanta a Kasar nan.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin sa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke karbar bakuncin Sakatare Janar na kungiyar Yawon bude ido ta majalisar dinkin duniya Mr.Zurab Polo-li-ka-shvili a fadar shugaban kasa dake villa a Abuja a yau Talata.
Ya ce mafi yawancin masu zuba jari na kasashen waje abinda suke maida hankali shine tsaron kasa kafin zuba jarin to kuwa yanzu an samu zaman lafiya a Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce sakamakon yanayin da tsaro ke ciki kafin hawan sa karagar mulkin kasar nan, babu ta yadda za’a yi masu zuba jari suyi sha’awar zuba jari a Najeria, an kasa gudanar da,taron kasa-da kasa na kan muhimmancin yawon bude ido a birnin tarayya Abuja kamar yadda ka yi a yanzu.
Da yake jawabi Mista Po-lo-li-ka-shvili ya yabawa kasar nan kan samun damar daukar nayin gudanar da taron, da ya hadar da Ministocin yawon bude ido na kasashen Afrika da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin yawon bude ido a duniya baki daya.
Shima a nasa jawabin ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammad cewa yayi wakilai 166 daga kasashen daban-daban da kuma Ministocin yawon bude ido daga kasashen Afrika 26 ne suka halarci taron wanda aka fara daga ranar 4 zuwa gobe 6 ga watan da muke ciki na yuni.