Connect with us

Labarai

An sanya wa sabon babban titin Legas zuwa Calabar sunan Tinubu

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta sanya wa babban titin gaɓar teku – da ya tashi daga Legas zuwa Calaba – sunan shugabana ƙasar Bola Tinubu.

Ministan ayyuka na ƙasar, David Umahi ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne domin nuna yabo ga hangan nesan shugaban ƙasar game da aiki.

Ya ce ma’aikatar ayyuka ta ƙasar ce ta yanke shawarar sanya wa titin sunan shugaban ƙasar, bayan tuntuɓar jagororin ma’aikatar.

Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, David Umahi ya ce Shugaba Tinubu ya amince da faɗaɗa aikin titin da kilomita 400.

Babban titin wanda ya ratsa jihohin Najeriya aƙalla tara ke bakin gaɓar ruwa zai an tsara zai laƙume kuɗi naira tiriliyan 15.

Titin mai tsawon kilomita fiye da 700 zai tashi daga Legas da kudu maso yammcin ƙasar, zuwa Kalaba da ke kudu maso kudancin ƙasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!