Coronavirus
Covid-19: An sassauta dokar kulle a jihar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa ta sassauta dokar kulle da zaman gida a jihar bayan shafe tsawon makon guda cikin halin zaman gida.
Cikin wani jawabi da Gwamnan jihar Ahmadu Umar Fintiri ya gabatar wa al’ummar jihar ta kafafan yada labarai ya ce a yanzu dokar kullen ta dawo daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
Har ila yau, gwamna Fintiri ya ce an samu karin mutum 1 da ya kamu da cutar da yammacin ranar Lahadinnan a jihar.
Wakilin mu Ahmad Tijjani Bawage ya rawaito mana cewa zuwa yanzu mutane 5 ne aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a jihar ta Adamawa.
You must be logged in to post a comment Login