Labarai
An tsaurara matakan tsaro a majalisun kasar nan dan hana zanga – zangar ma’aikata
Hukumomin majalisun kasar nan sun baza jami’an tsaro a sassan majalisun biyo bayan kudirin ma’aikatan majalisun na gudanar da zanga-zanga.
Zanga-zangar wadda ma’aikatan majalisun za su gudanar biyo bayan rashin biyan su kudaden albashi da ariya din su daga shekarar 2019 zuwa yanzu, da yawan su ya kai naira biliyan uku da biliyan daya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni harabar majalisun ya cika makil da jami’an tsaro don hana zanga-zangar ta su kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
Tuni dai shugaban kungiyar ma’aikatan majalisun Salisu Zuru ya bayyana matakin da suka dauka a matsayin abina ya saba da ka’ida.
You must be logged in to post a comment Login