Labarai
An yaye manyan sojoji 1,142 a kwalejin Jaji
Kwalejin horas da manyan hafsoshin sojojin kasar nan da ke Jaji a jihar Kaduna ta yaye jami’ai 1,142 bayan sun kammala karbar horo na musamman, domin taimakawa yaki da ta’addanci a kasar nan.
Babban hafsan sojojin kasa na kasar nan Laftanar Janar Tukur Buratai, wanda ya kasance babban bako a wurin bikin yaye jami’an, ya alkawarta samar wa jami’an walwala da kuma daga likkafarsu, domin karfafa musu gwiwa wajen gudanar da aikinsu.
Janar Buratai ya bukaci jami’an da su yi amfani da dabarun da suka koya wajen ganin an kawo karshen kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta musamman ma arewacin kasar.
Sannan ya gargade su da su kaucewa yada ayyukansu a shafukan sada zumunta, kasancewar akwai dokokin da aka shimfida na yadda ya kamata su rinka yin ta’ammali da shafukan.
Tun da fari da yake na sa jawabin, babban kwamandan kwalejin ta Jaji Manjo Janar Kelvin Aligbe, ya ce wannan shi ne karo na biyu da kwalejin ke yaye jami’ai na musamman kan dabarun yaki da kuma kakkabe ayyukan ta’addanci.
You must be logged in to post a comment Login