Labarai
An yi jana’izar Marigayi Aliyu Abubakar Getso

Da safiyar yau ne aka gudanar da jana’izar tsohon ma’aikacin gidan Radio Freedom Marigayi Aliyu Abubakar Getso wanda ya rasu da Asubahin yau Lahadi a nan Kano.
Kafin rasuwarsa Malam Aliyu Abubakar Getso,ta yi aiki a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano da Gidan Radiyon gwamnatin Kano kana nan Freedom Radio sai Vision FM kana daga bisani ya yi aiki da Premier Radio.
A zantawar wakilinmu Auwal Hassan Fagge da wasu cikin waɗanda suka halarci jana’izar, tsohon shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa NUJ shiyyar Kano Kwamared Abbas Ibrahim, ya bayyana kaɗuwarsa bisa rashin.
Shi ma a nasa ɓangaren makwabcin ga marigayin wanda shi ma ya kasance cikin masu gabatar da shiri A Freedom Radio Malam Babangida Umar, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi.
Marigayi Aliyu Abubakar Getso, ya rasu ya na da shekaru 69 bayan da ya yi fama da rashin lafiya inda ya bar Mata 3 da ƴaƴa 24 jikoki kuma 34.
You must be logged in to post a comment Login