Kiwon Lafiya
Ana ci gaba da duba marasa lafiya ta wayar hannu a Kano
Kungiyar dake wayar da kan al’umma da tallafawa mabukata kan cutar Covid-19 wato CORA, ta ce, za ta ci gaba da duba marasa lafiya kyauta da kuma basu shawarwari domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka ta wayar tarho musamman a wannan lokaci na kulle.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar Bashir Suwaid ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Rediyo Freedom da safiyar yau Litinin.
Bashir Suwaid ya ce, daga lokacin da aka kafa dokar kulle a fadin jihar Kano saboda cutar Corona, kungiyar ta raba tallafi ga mabukata a yankunan kananan hukumomin Kano guda biyar ga mutane sama da dubu daya da dari hudu.
Dakta Najib Usman wanda daya ne daga cikin likitoci a kungiyar ta CORA cewa yayi, hawan jini da ciwon suga da kuma matsalar mata masu juna biyu na daga cikin manyan cututtuka da suka warware matsalolinsu.
Kungiyar ta CORA ta kuma sha alwashin ci gaba da gudanar da ayyukanta domin tallafawa al’umma.
You must be logged in to post a comment Login