Coronavirus
Ana cigaba da gwajin Corona gida-gida a Kano
Gwamnatin jihar Kano tace ta fito da tsarin bi gida-gida don daukar samfurin gwajin cutar sarke numfashi ta Covid-19, yayinda take ganin hakan zai taimaka wajen magance yaduwarta a tsakanin al’umma.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a taron kaddamar da shirin gwajin cutar, wanda ya gudana a unguwar Wambai dake karamar hukumar Gwale.
Gwamna y ace akwai bukatar magance yaduwar cutar Covid-19 a tsakanin al’umma, wanda hakan ne ya sanya gwamnatinsa bullo da shirin gwaji cutar gida-gida.
Tun farko a nasa jawabi yayin taron, daya daga cikin jami’an kwamitin kar ta kwana kan yaki da annobar Covid-19 a jihar Kano, Dakta Tijjani Hussain ya ce a yanzu haka sun fara gwajin cutar gida-gida a karamar hukumar Birni da kewaye.
Wakiliyar Freedom Radio a fadar gwamnatin Kano Zahra’u Nasir ta ruwaito Dakta Hussain na cewa a gwajin da suka fara yi sun gano cewa ana samun raguwar masu dauke da cutar Covid-19 a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login