Kiwon Lafiya
Ana iya magance cutar kuturta- Ma’aikatar lafiya
Hukumar yaki da cutar tarin fuka da kuturta da kuma gymbon ciki ta kasa a Nijeriya ta ce kuturta cuta ce da za a iya magance ta tun kafin ta yi kamari, ta hanyar amfani da magungunan kashe kwatoyin cuta.
Shugaban hukumar Dr Chukwuma Anyaike ne ya bayyana hakan ga menma labarai jiya a Abuja, yayin taron bikin ranar yaki da cutar kuturta ta duniya da aka gudanar jiya.
Dr Chukwuma Anyaike ya ce an samar da magungunan kashe kwayoyin cutar da ke haddasa kuturta a duniya, wadda ake fatan ganin karshenta daga nan zuwa shekarar 2035.
Majalisar dinkin duniya ce ta ware duk ranar lahadin karshe ko wane wata domin gudanar da bikin, da nufin fadakar da al’umma hanyoyin kare kai daga cutar kuturta.
Taken bikin na bana shi ne a tashi tsaye don kawar da cutar kuturta.
Rahoto: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
You must be logged in to post a comment Login