Kiwon Lafiya
Ana samun karuwar masu ciwon kunne a Kano: Dakta Mustapha Sa’idu Salihu
Wani likita a sashen kula da lafiyar kunne magkwgaro da hanci a asibiti kwararru na Murtala Muhammad dake Jihar Kano ya bayyana cewa saka tsinke da wasu mutane keyi da sunan sosa kunne, ko kuma saka wani abu mai kaifi a cikin kunnen na haddasa ciwon kune.
Dakta Mustapha Sa’idu Salihu ne ya bayyana hakan a wani bangare na bikin rana kunne ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware, da akeyi duk ranar uku ga watan Maris na kowace shekara a matsayin rana kula da lafiyar kune.
Likitan ya kara da cewa ‘yawaita zama guraren dake da sauti mai karfi na jawo kurumta musamman ga wadanda suke yawaita jin kida a babbar sifika, ko amfani da na’u’rar jin sauti, wato iyafes’.
A don hakan Dakta Mustapha ‘ya ja hankali al’umma da su rinka zuwa ana duba lafiya kunnen su duk shekara’ don gujewa matsala.
A wani bangare na bikin ranar kuma, an gudanar da duba masu matsalar kunne kyauta, tare kuma da basu magunguna a asibiti kwararru na Murtala Muhammad din a yau.
You must be logged in to post a comment Login