Labarai
Ana tsaka da tantance shugaban hukumar NCC ta kasa
Majalisar datijjai na tsaka da tantance shugaban hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa ta kasa NCC farfesa Umar Danbatta a wa’adin mulki karu na biyu.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakakin hukumar Ikechukwu Adinde ya fitar a dazun nan.
A dai watan Yunin da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada farfesa Umar Danbatta na shekaru 5 a matsayin shugaban hukumar ta NCC.
Shi ne mutum na farko da aka nada ya jagoranci hukumar tun bayan nada shi a watan Agustan shekara ta 2015.
A ya yin tantancewar farfesa Umar Danbatta ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar tun kama aiki a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 2015.
NCC:wayar salula fiye da miliyan casa’in ne basu da rijistan layukansu
Hukumar NCC ta musanta cewar mazauna kusa da karfunan sadarwa ka iya kamuwa da cutuka
Ibrahim Oloriegbe Tinubu wanda manba ne a kwamitin tantace shugaban hukumar ta NCC da ya wakilci shugaban kwamitin y ace tantancewar ya zo dai-dai da sashi na 8 karamin sashi na 1 da na 4 na kundin tsarin mulkin da ya kafa hukumar ta NCA na shekara ta 2003.
You must be logged in to post a comment Login