Kiwon Lafiya
Ana wata ga wata: Akwai yiwuwar Ebola ta ɓulla a Najeriya – NCDC
Cibiyar daƙile yaɗuwar cutuka ta ƙasa NCDC ta ce, akwai yiwuwar ɓarkewar annobar Ebola a ƙasar nan.
Hakan na cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar ta shafinta na intanet mai ɗauke da sa hannun shugabanta Dr. Chikwe Ihekweazu.
Hakan dai na zuwa ne bayan da ƙasar Guine ta shiga fafutukar kawar da cutar daga ƙasar.
A ranar 14 ga watan Fabrairun da muke ciki ne ƙasar Guinea ta sanar da ɓarkewar cutar ta Ebola a ƙasar, lamarin da ya haifar da mace-macen jama’a a yankin N’zerekore na ƙasar.
NCDC ta ce, la’akari da kusancin Najeriya da Guinea ya sanya ta fitar da wannan sanarwa.
Saboda haka ta shawarci al’umma da su rinƙa wanke hannayensu da ruwa da sabulu, sannan a kaucewa ta’ammali da dabbobin daji.
Ana kamuwa da cutar Ebola ne, ta hanyar mu’amala da mai cutar ko taɓa jikinsa, ko guminsa, ko kuma gawarsa.
Haka ma ana kamuwa da cutar ta hanyar amfani da kayan marmari da Jemage ko Birrai suka yi amfani da shi.
You must be logged in to post a comment Login