Labarai
Ana zargin Gwamnatin Nijeriya na cigaba da bada tallafin man fetur
Rahotanni na nuni da cewar Gwamnatin Najeriya ta ci gaba da biyan tallafin man fetur, inda ko a watan Agustan da ya gabata ma, sai da ta biya Naira biliyan 169 da miliyan dari 4, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Rahoton dai ya yi nuni da cewa duba da karuwar farashin man da aka samu a kasuwannin duniya da ya haura dala 95 akan kowacce ganga, da gwamnatin tarayyar ba ta biya kudaden tallafin ba, a yanzu ana sayen man fetur din a fadin kasar nan akan kusan naira dubu daya kowacce lita.
Amanallah Ahmad Muhammad, mai sharhi akan al’amuran yau da kullum na ganin cewa ko da an samu karuwar farashin a kasuwannin duniya ba zai zama dalilin da zai sa a samu karin farashin man ba, sai dai ma ya zama riba ga kasar a cewar sa.
A cewarsa ‘duk duniya ba kasar da suke shan man fetur da tsada sama da yadda ‘yan Nijeriya suke sha, wanda ya ce gwamnati idan taga dama zata saukaka lamarin nan da kanta’.
Rahoton: Sunusi Shu’aibu Musa
You must be logged in to post a comment Login