Labaran Kano
Ana zargin jami’in lafiya da yiwa bazawara fyade a Kano
Kotun shari’ar musulunci dake zamanta a garin Madobi dake nan Kano ta cigaba da shari’ar jami’in ladiyar nan Sani Dahiru wanda ake zargi da yiwa wata bazawara fyade.
Tun da farko wata bazawara mai suna Fatima Yusuf ce tayi karar Sani Dahiru, bisa zargin ya hilace ta ya zuba mata wani sinadari mai juyar da tunani acikin shayi.
Bayan ta sha shayin ne, sai bacci ya kwashe ta, shi kuma yayi lalata da ita.
Sai dai a lokacin da taji alamun juna biyu sai taje asibiti domin a duba lafiyar ta, sai ta iske Sani Dahirun shi ne mai duba marasa lafiya a asibitin, daga nan ne kuma sai ya bata wani magani, sannan yace da ita ciwon sanyi ne yake damun ta, ya sallame ta.
Bayan tasha maganin ne, sai ya haifar mata da sabuwar wahala ta dan loakaci, domin kuwa ashe maganin zubar da ciki ne.
Wakilin mu Yakubu Musa Kanwa ya rawaito mana cewa Fatima Yusuf tayi sabon aure, a nan ne kuma sabon mijin ya gane tana da juna biyu sannan ya sallameta.
A yayin zaman kotun na jiya Talata wanda ake zargi Sani Dahiru ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
A don haka alkalin kotun mai shari’a Bello Musa Khalid ya dage wannan shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Afrilu mai kamawa, tare da umarnin ajiye wanda ake zargi a gidan gyaran hali.
You must be logged in to post a comment Login