Connect with us

Labarai

Ana zargin kama wani mutum kan ihun rashin ruwa da wuta a ziyarar gwamnan Neja

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Hamisu Abdullahi, bisa zargin yin ihu da cewa “babu ruwa, babu wuta” yayin ziyarar gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago a garin Suleja.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin kokarin tayar da hankali da kuma kawo cikas ga ayyukan gwamnati a lokacin ziyarar Sallah.

 

Ya kara da cewa an tsare mutumin a sashen binciken manyan laifuka da ke Minna a ranar 20 ga watan Maris, kafin daga bisani a ba shi beli yayin da ake ci gaba da bincike.

 

A cewar wani dan uwansa, Haruna Abdullahi, an sako mutumin ne a ranar Talata bayan shafe kwanaki biyar a tsare.

 

Sai dai har yanzu ana zargin cewa kama mutumin na da alaka da umarnin gwamnan, duk da cewa babu wata cikakkiyar hujja da ke tabbatar da hakan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!