Manyan Labarai
Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro
Kungiyar Inuwar Musulman Najeriya wato Islamic Forum of Nigeria, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya rubanya kokarinsa wajen kawo karshen matsalar tsaro dake addabar yankin Arewacin kasar nan.
Mai binciken kudin kungiyar ta kasa Malam Sale Adamu Kwaru, ne bayyana hakan a taron kungiyar na shekara-shekara da ya saba gudana, wanda akayi a nan Kano.
Malam Sale Kwaru, ya ce ba yadda za samu cigaba mai dorewa matukar babu ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar kasar nan.
Labarai masu alaka.
Kyautatawa malamai ya zama wajibi- Shekarau
Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami
Ya kuma ce jihohin Arewacin kasar suyi koyi da takwarorin su na kudanci wajen aiyyukan cigaba, tare da samar da tsayayyun manufofi .
Taron ya samu halartar malamai daga sassan kudancin kasar nan da sauran gurare suka halarci taron domin lalubo bakin zare kan matsalolin tsaro dake damun kasar nan, kamar yadda wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, ya ruwaito mana.
You must be logged in to post a comment Login